1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar kawo karshen yakin Ukraine a Abu Dhabi

January 25, 2026

Shugaban Ukraine, Zekenskyy ya ce tattaunawa a rana ta biyu tsakanin masu shiga tsakani na Amurka da Rasha da ke gudana a birnin Abu Dhabi ta kasance mai cike da fa'ida.

Taron zaman lafiya kan yakin Ukraine a birnin Abu Dhabi
Taron zaman lafiya kan yakin Ukraine a birnin Abu DhabiHoto: UAE Government/REUTERS

Shugaba Zelenskyy ya ce an tattauna a kan abubuwa da dama a zaman sulhu a birnin Abu Dhabi, sai dai an fi mayar da hankali kan matakan kawo karshen yakin na Ukraine. 

Wakilan da suka halarci zaman tattaunawar ana sa ran su mika rahoto ga gwamnatocinsu domin ganin matakai na gaba da za a dauka. Zelenskyy ya ce za a gudanar da wasu tarurruka a farkon makon gobe. Wani mai magana da yawun gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce tattaunawar ta fitar da batutuwa na kai tsaye a daftarin shirin zaman lafiya da Amurka ta gabatar. 

Karin bayani: Saura kiris Ukraine ta samu zaman lafiya - Trump 

Kawo yanzu babu wani cikakken bayani kan abin da aka tattauna, sai dai rahotannin a baya sun yi nuni da cewa, batun ikon mallakar yankuna aka fi mayar da hankali a kai. Rasha ta matsa lamba sai Ukraine ta janye dakarunta daga yankunan gabashin Dombas da Moscow ba ta da iko da shi, sai dai Kyiv ta ki amincewa da wadannan bukatun. 
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW