Tattaunawar komitin sulhu akan koriya ta Arewa
October 11, 2006Ayanzu haka wakilan komitin sulhun mdd na gudfanar da taro a birnin new york din Amurka,domin laakari da matakan ladabtar da koriya ta arewa ,sakamakon ikirarinta na gwajin makamin nuclearnta na farko.Kakakin maaikatar harkokin waje na koriyan ,yace pyongyang zatayi laakari da kowane mataki na takunkumi aka kaddamar akanta,amatsayin yaki.Daya magana a bayan fagen wannan taro nayau,sakatare general na mdd Kofi Annan ,ya yi kira ga gwamnatin Pyongyang datayi taka tsantsan.A yayinda a hannu guda kuma kuma Japan ta sanar da haramtawa jiragen ruwa na Koriya ta arewa shiga dukkan tashoshinta,tare haramta shigar da dukkan kayan da suka fito daga wannan kasa mai tsarin mulkin kommunisanci.Bugu da kari a sanarwa data gabatar,gwamnatin Japan din tace ta harantawa dukkan yan koriya ta arewan shiga kasarta,banda wasu yan kalilan.