Tattaunawar Rasha da Japan
February 11, 2011![](https://static.dw.com/image/6182381_800.webp)
A ranar 11 ga watan Fabrairu ƙasashen Rasha da Japan za su shiga tattaunawa domin kawo ƙarshen yaƙin cacar baki da suke yi akan wasu jerin tsibirai. Ganawar da za a yi tasakanin ministan harkokin wajen Japan da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov a birnin Moscow ta zo ne bayan da suka shafe shekaru suna taƙaddama akan tsibiran Kuril da Japan ta bayyanar a matsayin mallakarta da Tarayyar Soviet ta mamaye a ƙarshen yaƙin duniya na biyu. Lavrov ya gargaɗi Japan da cewa ba za a amince da take-takenta ba . Wannan taƙaddamar da ƙasashen ke yi a tsakaninsu ita ce ta hana su sanya hannu akan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin duniya na biyu a hukumance. Shugaban Rasha, Dmitry Medvedev ya ba da shawarar keɓe tsibirin a matsayin yankin walwalar kasuwanci domin jan hankali masu saka jari daga Japan akan kyawawan sharuɗa. A ɗayan hannun kuma buƙatar Japan ita ce samun kafar samar da iskar gas daga wannan yanki.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu