1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar rikicin Libiya a Alƙahira

April 14, 2011

Wakilan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa a birnin Alƙahirar sun ce ya zama wajibi a yi amfani da diplomasiyya wajen ciyo kan rikicin Libiya

Ban Ki-MoonHoto: AP

Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na cigaba da ganawa a birinin Alƙahira saboda ƙara matsin ƙaimi domin a tsagaita wuta a Libiya. Babban sakataren Majalisar Ban Ki-Moon ya ce ƙungiyoyin sun damu ƙwarai sakamakon ta'azarar da da tashe-tashen hankulan ke yi a ƙasar, kuma ya ce majalisar zata sake aikawa da manzo na musamman wanda zai cigaba da tattaunawa da ɓangarorin biyu.

"akwai mutanen da ke fama da ƙarancin ruwa da abinci da sauran kayan buƙatun yau da kullun da suka wajaba, kuma mun damu ƙwarai da makomar 'yan ƙasashe masu tasowa, waɗanda ke gudun hijira da kuma baƙin haure da suka maƙale a wuraren da ke fama da yaƙi"

Wakilai a taron, waɗanda suka haɗa da babbar kantomar da ke kula da harkokin wajen Turai, Catherin Ashton, da shugaban ƙungiyar haɗin kan Larabawa Amr Moussa da takwarar sa na ƙungiyar Tarayyar ƙasashen Afirka Jean Ping, suma sun goyi bayan ƙudurin na neman tsagaita wutan a Libiya kuma sun buƙaci da a tabbatar da tsaron fararen hular ƙasar a kuma kai masu agaji yadda ya kamata. A yayin da ƙungiyoyin ke wannan ganawar, masu boren ƙin jinin gwamnati, sun gudanar da wani jerin gwano a gaban shelkwatar ƙungiyar haɗin kan Larabawan, inda suka yi wani taho mu gama da ƙungiyoyin da ke goyon bayan Gaddafi. Mutane da dama sun yi rauni.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Ahmed Tijjani Lawal