1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Tattaunawar samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Binta Aliyu Zurmi
March 3, 2024

Manyan jami'an diplomasiyyar kasashen Amurka da Qatar da bangaren jagogorin kungiyar Hamas na ci gaba da tattaunawa a kasar Masar a kan batun samar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni 6.

Hamas Anführer Saleh al-Arouri
Hoto: Ibrahim Ezzat/Zuma/IMAGO

Ana dai kokarin ganin an cimma kwakwarar yarjejeniya kafin ranar 10 ga wannan watan na Maris da al'umma Musulman duniya ke sa ran fara azumin watan Ramadana. 

Yarjejeniyar da ake sa ran Isra'ila ta amince da ita na da nufin musayar fursunoni da ke makare a gidan yarin Isra'ila da kuma 'yan Isra'ila da Hamas ke ci gaba da garkuwa da su gami da janye sojojin Isra'ila daga Gaza da kuma bada damar shigar da kayan agaji.

Wannan tattaunawar dai na zuwa ne a yayin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a Gaza da ma kokarin neman kutsa kai a yankin Rafah.

Sama da mutum 30,000 ne aka tabbatar da mutuwar su tun bayan da wannan yaki ya barke. Isra'ila na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga manyan kawayenta na ganin ta tsagaita wuta.