Tantama kan makomar Yemen
June 15, 2015 Bangarori biyu masu gaba da juna a kasar Yemen za su taru a karon farko a Geneva a ranar Litinin din nan a kokarin kawo karshen zubar da jini a fafatawar da a ke yi tsakanin bangaren Houthi da ke zama 'yan Shi'a masu samun goyon bayan kasar Iran, da sojoji da ke mara baya ga gwamnatin Abedrabbo Mansour Hadi.
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya da ke shiga tsakani a shirin na sulhu Ismail Ould Cheikh Ahmed ya ce za su ga yadda fara wannan tattaunawa za ta yi tasiri wajen kawo karshen yaki da ya jawo kisan fiye da mutane 2,500, abin da ya bude kofa ga shirin neman agajin kasa da kasa ga dubban al'umma da yaki ya ritsa da su.
A cewar wasu masharhanta dai da wuya a wannan tattaunawa a cimma wata nasara kasancewar tawagogin ba ma za su zauna bane wuri guda dan fahimtar juna.