1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar tsagaita wuta a Gaza

Usman Shehu Usman
August 15, 2024

Bayan jimawa da aka yi ana jiran fara sabon zagayen magance rikicin da ya lakume rayukan jama'a musamman fararen hula yanzu daga karshe an fara zaman tattaunawar samar da tsagaita wuta a Gaza.

Gazastreifen Gaza | Zerstörung nach israelischem Angriff auf Schule
Hoto: Omar Al-Qattaa/AFP/Getty Images

Tattaunawar wace aka fara a Doha babban birnin kasar Katar ana sa ran za ta samar da tsagaita wuta da kuma sakin mutanen da ake garkuwa da su. Daga cikin wadanda za su halarci tattaunawar har da shugaban leken asirin Isra'ila da takwaransa na Amirka hadi da firaministan Katar.

Tun bayan harin bakwai ga watan Oktoba na shekarar 2023, da Hamas ta kai, an sha zaman tattaunawa amma kuma babu daftari daya da aka amince da shi, yayin da a can Gaza kuma ake cigaba da rasa rayukan jama'a, inda yanzu alkaluman ma'aikatar kiwon lafiya a Gaza ke nuna cewa, kusan mutane dubu 40 suka mutu tun fara yakin.