1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar warware rikicin daya taso a tsakanin Russia da Ukraine

January 2, 2006

Wasu jakadun kasashen Turai dana kasashen Japan da Amurka na gudanar da wata tattaunawa a tsakanin su da shugaban kasar Ukraine, Viktor Yushchenko a babban birnin kasar wato Kiev.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa shugabannin na tattauna hanyoyin warware rikicin hayakin gas ne dake a tsakanin kasar ta Ukraine da kuma Russia.

Wannan dai rikici a tsakanin kasashen biyu ya samo asali ne bayan da mahukuntan na Russia suka ce zasu kara farashin hayakin gas din ga kasar Ukraine, wanda kuma tuni mahukuntan na Ukraine sukayi watsi da wannan aniya, inda a yanzu ta kai ga katse hayakin gas din da kasar ta Russia take sayarwa kasar ta Ukraine

A yayin da rikicin hayakis gas a tsakanin kasar Russia da Ukraine ke kara daukar sabon salo, ministan tattalin arziki na Jamus, wato Michael Glos cewa yayi wannan rikici ba zai shafi katsewar hayakin gas din daga Russia izuwa Jamus ba.

Rahotanni dai sun nunar da cewa kashi 35 daga cikin hayakin gas din da Jamus take amfani dashi, tana sayen sane daga kasar ta Russia.

.