1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tautaunawa da hukumar makamashi ta duniya da Iran

MamaneAugust 24, 2012

Hukumar kasa da kasa ta makamashi na tautaunawa da kasar Iran a kan shirinta na nukleya.

(FILES)--A picture shows the reactor building at the Russian-built Bushehr nuclear power plant in southern Iran on August 21, 2010 during a ceremony initiating the transfer of Russia-supplied fuel to the facility after more than three decades of delay. Iran's atomic chief has said a small leak in a pool beside the Bushehr reactor has delayed the start-up of the nuclear plant, the official IRNA news agency reported on October 4, 2010. AFP PHOTO/ATTA KENARE (Photo credit should read ATTA KENARE/AFP/Getty Images)
Hoto: AFP/Getty Images

  A wannan juma'ar ne kasar Iran zata sake komawa kan teburin shawara a ci-gaba da tautaunawa da ta ke yi da hukumar makamashi ta kasa da kasa wato AIEA a kan batun shirinta na nukleya.Tun can farko dai, wata tautaunawa da a ke yi tsakanin kasar ta Iran da kuma wasu kasashe da suka hada

Amirka,Rasha,Chana,Faransa,Birtaniya da kuma Jamus sun ci karo da rashin fahimtar juna inda kasashen  ke zargin hukumomin Teheran da sarrafa makaman nukleya a asirce,yayinda kasar ta dage a kan shirinta na mukamashin farar hulla ne. Wannan sabuwar masayar yayu ta zo ne a daidai lokacin da kasar Isra'ila ke yawaita barazanar kaiwa kasar ta Iran hari muddun bata dakatar da shirin nata ba.


Mawallafi: Issoufou Mamane

Edita:       Abdoullahi Tanko Balla