1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar kasashen Larabawa ta isa Siriya

December 23, 2011

Ko bayan isar tawagar kungiyar kasasen Larabawa a Siriya gwamnatin kasar ta dauki matakan murkushe masu boren neman sauyi

'Yan zanga-zanga a birnin HomsHoto: AP

Tawagar farko ta 'yan sa ido daga kungiyar kasashen Larabawa ta isa kasar Siriya domin share ma wata babbar tawwagar da za ta kunshi kwararrun 150 hanyar zuwa kasar kafin shekara mai kamawa. 'Yan adawa a kasar ta Siriya sun ba da rahotannin da ke nuni da cewa duk da cewa wannan tawwaga ta isa kasar gwamnatin ta ci gaba da daukar matakai masu tsauri domin murkushe masu boren nuna adawa da ita. A ranar Alhamis 22-12-2011 an fuskanci mutuwar mutane da dama mafi yawansu a birnin Homs. Hakazalika a biranen Idlib da Daraa an samu wadanda gwamnatin ta dauki matakan ba sani ba sabo akansu. 'Yan rajin kare hakkin bil Adama sun ce gwamnatin kasar ta Siriya tana kokari ne ta kawo karshen zanga-zangar nuna adawa da ita kafin isar babbar tawwagar a kasar. Masu rajin kare hakkin bil Adama sun kiyacse cewa sama da mutane 6000 suka rasa rayukansu tun bayan ta da bore a kasar a watan Maris.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi