1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Yan kallon zabe za su je Venezuela

Abdoulaye Mamane Amadou
October 15, 2021

Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta aika tawagar kwararrun zabe zuwa Venezuela dan sanya idanu kan yadda za a gudanar da zabukan kananan hukumomi da na gwamnoni na karshen watan gobe.

Mexiko | Celac-Gipfel in Mexiko-Stadt | Nicolas Maduro
Hoto: Agencia Venezolana de Noticias/Xinhua/picture alliance

Kasar Venezuelan ce dai ta bukaci Majalisar Dinkin Duniyar ta aike da tawagar. Sai dai sabanin yadda ta saba a wannan karon, tawagar kwararrun zaben za ta sa ido ne kawai kafin daga bisani ta gabatar da cikakken rahoton yadda ya wakana. Ita ma dai kungiyar Tarayyar Turai ta ce ta cimma wata yarjejeniya da Venezuela domin tura tawagar masu sanya ido a zaben, wanda ke zama tamkar wani zakaran gwajin dafi biyo bayan amincewar da jam'iyyun adawa suka yi  na shiga a dama da su a wannan karo sabanin yadda suka yi ta biris da zabukan da suka gabata na shekarar 2018 da na 'yan majalisun dokokin kasar na shekarar da tagabata.