1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar Najeriya ta yi cikar kwari a taron COP29

Ubale Musa MAB(AMA
November 13, 2024

A daidai lokacin da ake cikin yanayi a Najeriya, tawagar kasar ta mamaye babban taron koli na sauyin yanayi da shugabannin duniya ke gudanarwa a birnin Baku na kasar Azerbaijan

Taron sauyin yanayi na kasa da kasa COP29 a birnin Baku na kasar Azerbaijan
Taron sauyin yanayi na kasa da kasa COP29 a birnin Baku na kasar Azerbaijan Hoto: Peter Dejong/AP/picture alliance

Duk da kace-nace da ya dauki hankali ciki da ma wajen tarayyar Najeriya kan yawan adadin 'yan tawagar da suka wakilci Najeriya a babban taron kare muhalli na duniya, a bana ma kasar ce ke da wakilai mafi yawa daga nahiyar Afrika a taron alkinta muhalli na duniya dake gudana a kasar Azarbaijan. A taron COP28 na Dubai wakilai 1.411 da suka fito daga sassa daban-daban ne suka tafi taron alkinta muhalli da sunan Najeriya.

Karin bayani : Rage amfani da makamashin da ba a sabuntawa

Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Gbemiga Olamikan/AP/dpa/picture alliance

A bana duk da ragin da aka gani, tawagar Najeriya da ta kunshi wakilai 436 a taron da ke gudana a birnin Baku na kasar Azarbaijan na daukar hankalin ragowar 'yan kasar, da ke zaman jiran cika alkawarin gwamnatin Tinubu na rage kashe-kashen kudin al'umma. Adawa da kashe kudin Najeriya maras adadi a shekarar 2023 ne ma ya tilasta gwamnatin alwashin kawo sauyi kan halartar taron na wannan shekara, matakin da Umar Saleh Anka, ya tabbatar da cewa, Najeriyar ta yi muhimmin gyara kan wakilcinta.

Karin bayani : Koma baya na yaki da kare muhalli a Kamaru

Taron sauyin yanayi na kasa da kasa COP29 a birnin Baku na kasar Azerbaijan Hoto: Peter Dejong/AP Photo/picture alliance

Ko da yake Najeriyar ita ce kan gaba da tafi yawan wakilai daga nahiyar Afirka, wanda hakan ya saba alkawarin ragin kashe makudan kudi a zuwa manyan tarukan kasashen ketare da hukumomi suka yi a baya wanda shugaban kasa ya sha alwashin cewar ba zai wuce mutum 25 ba a duk wasu tafiye-tafiyensa na waje, haka kuma mutum 20 ga mataimakinsa. Sai dai da take mayar da martani, fadar shugaban kasa ta sanar da cewa mafi yawan masu halartar taron na kare muhalli a Azarbajan ba su tafi taron a cikin aljihun gwamnati ba. Najeriya na zaman kasa ta tara mafi yawan mahalarta taron na bana, kuma ta farko a nahiyar Afirka da wakilai 436, sai Uganda mai wakilai 412.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani