Tawagar sa ido ta ƙasashen larabawa ta isa ƙasar Siriya
December 27, 2011Tawagar sa ido ta ƙasashen larabawa na shirin fara duba yarjejeniyar da aka cimma da nufin kawo ƙarshen watanni na tarzomar Siriya da ya yi sanadiyar mutuwar dubban jama'a. Masu rajin kare haƙƙin bil Adama na Faransa da kuma Siriya sun buƙaci tawagar ta mutane hamsin wadda kuma ta sauka Siriyar 'yan sa'oi da suka wuce ta zarce kai tsaye zuwa garin Homs inda mazauna yankin suka ce an kashe mutane 20 a jiya Litinin. Ita ma ƙungiyar nazari da kare haƙƙin bil Adama ta Syrian wadda ke da mazauninta a birnin London ta ce sojojin gwamnatin Siriya sun yiwa garin Baba Amr ƙawanya. Tashin hankula sun ƙaru bayan da mutane 44 suka rasa rayukansu a wasu hare haren bama bamai biyu da aka kai wasu gine ginen gwamnati a birnin Damascus a ranar juma'ar da ta gabata. A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya aƙalla mutane 5,000 ne aka kashe tun bayan da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad ta fara dirar mikiya akan masu zanga zangar da ita watanni tara da suka wuce.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi