1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Wakilan Amurka na shirin zuwa Pakistan

April 24, 2026

Amurka ta aike da tawaga zuwa Pakistan domin halartar zagaye na biyu na tattaunawa da Iran a kokarin kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya.

Pakistan Islamabad 2026 | Plakat vor den US-iranischen Verhandlungen
Hoto: Ilya Ryzhov/ITAR-TASS/IMAGO

Tawagar wakilan Amurka da ta kunshi Steve Witkoff da Jared Kushner za ta nufi kasar Pakistan a ranar Asabar, domin ci gaba da tattaunawa da Iran, da nufin kawo karshen yakin yankin Gabas ta Tsakiya wanda ya yi garkuwa da duniya.

Kakakin fadar White House Karoline Leavitt ce ta tabbatar da hakan ga giddan talabijin na Fox News, inda ta ca tawagar za ta halarci zagaye na biyu na tattaunawa da wakilan Iran a birnin Isalamabad, sai dai a wannan karo mataimakin shugaban Amurka JD Vance ba zai samu zarafin halartar zaman ba.

Karoline Leavitt ta kuma kara da cewa akwai kyakkyawan fata kan cewa tattaunawar ta wannan karo za ta kasance mai amfani kuma mai cike da nasara.

Ana dakon isar jami'in diflomasiyyan Iran Islamabad

Wannan na zuwa ne dai a daidai lokacin da majiyoyi daga Pakistan suka sanar da cewa ana sa ran ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi zai isa birnin Islamabad fadar gwamnatin kasar a daren Juma'ar nan, sai dai ba tare da fayyyace dalilin zuwan nasa da kuma wadanda zai gana da su ba.

Tsagaita wuta a Lebanon na tangal-tangal