Tawagar wakilan Amurka za ta koma Pakistan
April 25, 2026
Fadar mulkin Amurka ta White House ta ce sabuwar tattaunawar da Steve Witkoff da surukin Shugaban Donald Trump Jared Kushner za su jagoranta za a yi ta ne ta keke da keke, sai dai daga bangaren Tehran sun ce babu wannan batun.
Tun a ranar Juma'a ne rahotannin suka tabbatar da isar ministan harkokin wajen Iran Abass Aragchi a kasar ta Pakistan. Kafar talabijin mallakin kasa ta ce ministan ba shi da wani shirin ganawa da Amurkawa, kuma Islamabad za ta ci gaba da zama mai shiga tsakanin don isar da sakonninsu.
Kakakin Iran ya ce Araghchi zai ziyarci kasashen Oman da Rasha bayan Pakistan dake kokarin kawo karshen yakin da Isra'ila da Amurka suka kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ranar 28 ga watan Fabrairu.
Karin Bayani:Rashin tabbas kan warware rikicin Iran