1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tawagar WHO ta isa lardin Ituri mai fama da Ebola a Kwango

May 29, 2026

Darakta Janar na WHO Tedros Ghebreyesus, ya kai ziyarar gani da ido Ituri kuma waje mafi hadarin kamuwa da Ebola a DRC.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Ghebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Ghebreyesus Hoto: Salvatore Di Nolfi/KEYSTONE/picture alliance

Tun da fari dai, kafofin yada labaran Kinshasa sun rawaito cewa nan gaba a yau ake sa ran Ghebreyesus zai kai ziyara lardin Ituri  da ke arewa maso gabashin DRC, a cikin wani yanayi na cikakken matakan kariya. A sakon da ya wallafa a shafinsa na X gabanin ziyarar, shugaban ya ce duniya na tare da al'ummar Kwango a wannan yanayi da suke ciki.

Karin bayani: Kasashe makwabtan DRC na fuskantar barazanar Ebola- WHO

WHO ta yi rajistar mutane 10 da suka kamu da cutar da kuma mutum 223 da ake zargin sun mutu, sakamakon kamawu da cutar Ebola tun bayan sake barkewar cutar a ranar 15 ga watan Mayu. Kazalika mutane sama da 1,000 sun kamu da cutar daga cikin alkaluman da aka tattara a ranar 24 ga watan Mayu.