Tawagogin Palestinu da Isra'ila sun kammalla taro a Amman ba tare da nasara ba
January 4, 2012An watse ba tare da cimma wani sakamakon a zo a ga ni ba, tsakanin Isra'ila da Palestinu, da kuma tawagar masu shiga tsakani a taron da su ka shirya jiya a birnin Amman na kasar Jordan.
Saidai bangarorin sun yi alkwarin komawa kan tebrun shawara ranar Juma'a mai zuwa.
Tun watan satumba na shekara 2010, tattanawa tsakanin Isra'ila da Palestinu ta shiga wani halin kiki-kaka, to amma a wannan karo inji ministan harkokin wajen Jordan ,Nasser Djude an dan samu cigaba:
"Dr Erekat da sunan tawagar Palestinu ya gabatarwa Isra'ila shawarwarin warware rikicin, kuma a karon farko Isra'ila ta karbi wannan shawarwari."
Shugaban Hukumar palestinawa Mahamud Abbas, ya dauki matakin kauracewa shawarwarin bayan da Isra'ila da kaddamar da wasu sabin gine-gine a yankunan Palestinu.
Mawwalafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu