Masana sun nemi a wadata mata da maganin tazarar haihuwa
October 16, 2019Talla
A rahoton da wata Mujallar BMJ and Reproductive Health Medical mai kula da kiddigar al'umma ta birnin New York ta fitar, ta ce kashi arba'in da hudu cikin dari na cikin da mata ke dauka a duniya a bisa kuskure ne.
Rahoton ya nunar da yadda bunkasar al'umma, ke kara bukatun abinci da makamashin girki dana ababen hawa, matsalolin da ke kara ta'azzara dumamar yanayin. Hasashe ya nuna cewa nan da shekaru biyu masu zuwa alkaluman al'ummar duniya zai haura zuwa Biliyan goma daga sama da biliyan bakwai da ke rayuwa yanzu, saboda haka tsarin iyali ya kasance sahun gaba a muradun shawo kan matsalar inji rahoton.