Tchiroma zai kalubalanci Paul Biya a zaben Kamaru
June 27, 2025
Issa Tchiroma Bakary, ya share tsawon shekaru 20 yana riƙe da mukaman minista a Kamaru. Amma kwatsam ya kawo karshen kawancen da jam’iyyarsa ta FSNC ke yi da gwamnatin Shugaba Paul Biya. A wani faifain bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya ce ya yi murabus ne saboda wahalhalun da al’ummar Kamaru suke fuskanta, wadanda ba zai iya jurewa ba.
Karin bayani: Shin matasa sun shirya shiga siyasar Kamaru?
Tchiroma ya ce na yi murabus ne don amsa kira da al'umma ke yi masa, inda ya ce: ‘’Na yi murabus a yau saboda kowa na da masaniyar cewa al’ummar Kamaru na fuskantar kalubalen, yawancin su ba sa iya biya wa kahunansu bukatunsu, al’ummar Kamaru sun kasance cikin tsoro da bacin rai da rashin tabbas game da rayuwarsu , lamarin da ya kai ga bishop uku 'yan Arewa suka nuna bacin rai kuma suka bukaci canji, a kan haka ne na amsa kiran al’ummar Kamaru daga Arewa, Kudu, gabashi zuwa yammaci’’
Tchiroma na neman kare muradun arewacin Kamaru
Murabus da tsohon kakakin gwamnatin Kamaru na tsahon shekaru 10 bai zo wa mutane da mamaki ba, ganin yadda a kwanakin baya, aka ji kalamansa da ke nuna shirin juya wa Shugaba Paul Biya baya, inda aka jiyo shi a birnin Garoua yana sukar kawancen shekaru 43 na mulkin Paul Biya, wanda ya ce bai amfane su da komai ba. Hasali ma, shugaban jam'iyyar FSNC, ya ce ba zai kara yi wa Paul Biya yakin neman zabe ba, wanda a ganinshi, shi ne musabbabin matsalolin jama'ar Arewacin kasar ta Kamaru.
Issa Tchiroma Bakary ya ce: ‘'Ina so ku gane cewa ni shugaban jam'iyyar siyasa ne, idan kana shugabantar jam'iyyar siyasa muna da maza da mata wadanda suka sadakar da rayuwarsu domin ganin cewa na kai su zuwa ga gaci, a kan haka ne idan na ga wani abin da zai sanya al'ummar da nake shugabanta cikin bakin ciki, dole na yi kira ga canji... A wannan lokaci, ba ni da wani zabi da ya wuce in saurari koke-koken al'umma''
Karin bayani: Jagororin Katolika sun shata sharadi ga masu neman shugabancin Kamaru
Wannan murabus ya sa Paul Biya, rasa wani babban jigo a yankin arewacin Kamaru da ake kallo a matsayin wani rumbun kuri’u, a daidai lokacin da ya rage watanni 4 a gudanar da zaben shugaban kasa. Wasu 'yan jam'iyyar masu mulkin kasar Kamaru ba su ji dadin abin da ya faru ba, yayin da murabus dib bai zo musu da mamaki ba
Tasirin Arewa a zaben shugaban kasar Kamaru
Sambo Djaloud, mai fafutukar wayar da kan al’ummar Arewa game da kawo canji a kamaru na ganin cewa, fasa kawance da jam’iyya mai mulki na iya karya kashin bayanta. Ya ce: ‘’Ai kullum abin da Paul Biya yake gaya mana shi ne, akwai kaso 70 % da wani abin da yake samu na kuri’un nan domin ya ci zabe, kaso 52% daga arewacin Kamaru ake samu’’
Karin bayani: Ina makomar Ilimin jami'a a Kamaru?
Fitowar Issa Tchiroma Bakary na zuwa ne yayin da guguwar siyasa ke kadawa a yankunan kasar biyu Arewa da Kudu musamman ma mahaifar shugaban kasa inda suka tayar da kayar baya da kira da a juya wa Paul Biya baya.