Mojtaba ya gargadi Amurka da Isra’ila kan mamaya
March 20, 2026
A wata sanarwa da jagoran addinin ya fitar a ranar sabuwar shekara a kasar, Ayatollah Mojtaba Khamenei, ya ce Tehran da kawayenta ba su da wata alaka da wadannan hare-hare. Ya zargi matakin da cewa babban yaudara ne.
Khamenei ya bayyana cewa makiyan Iran, ciki har da Amurka da Isra'ila, na fuskantar kalubale a yakin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya. Sabon jagoran ya ce "Hadin kan da aka samu tsakanin ‘yan kasar Iran ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarori a fagen daga."
Tun bayan tabbatar da shi a matsayin magajin mahaifinsa da harin ya Amurka ya kashe, har yanzu ba a ga Mojtaba a bainar jama'a ba.
Kungiyar kwancen tsaro ta NATO, ta ce ta kwashe dukkannin dakarunta daga kasar Iraki, amma Shugaba Donald Trump ya caccaki kungiyar da cewa "mara tasiri" sakamakon watsi da bukatarsa na kai agaji mashigin Hormuz. Bayanai na cewa kusan jiragen dakon danyen mai 100 sun wuce ta mashigar Hormuz bayan fara yakin.