1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Thiam ya ce zai kalubalanci soke takarsa a kotun ECOWAS

Mouhamadou Awal Balarabe
April 23, 2025

Wata kotun Abidjan ta yi amfani ne da sashe na 48 na dokokin zama dan kasa wajen kawar da takarar Tidjiane Thiam, wanda ya ce duk wani dan Côte d' Ivoire zai yi asarar matsayinsa da zarar ya samu fasfo na wata kasa.

Tidjane Thiam ne jam'iyyar PDCI ta tsayar takara a zaben 2025 a Côte d' Ivoire
Tidjane Thiam ne jam'iyyar PDCI ta tsayar takara a zaben 2025 a Côte d' IvoireHoto: Ennio Leanza/KEYSTONE/picture alliance

Madugun adawa na kasar Côte d' Ivoire Tidjane Thiam ya ce zai shigar da kara gaban kotun ECOWAS/CEDEAO don kalubalantar hukuncin korar takararsa a zaben shugabancin kasa na watan Oktoba mai zuwa. A yayin wata tattaunawa da ya yi da kanfanin dullancin labaran Faransa AFP,  Mista Thiam ya ce shi ne dan takara daya tilo na jam'iyyarsa ta PDCI, wacce ba ta tanadi maye gurbinsa da wani dan takara ba.

A ranar Talata ne kotun Abidjan ta cire sunan Tidjane Thiam daga cikin jerin wadanda suka yi rejistan kada kuri'a, inda ta ce ya rasa takardar zama dan kasar Côte d' Ivoire tun bayan da ya dauki fasfon kasar Faransa, duk da cewa ya mayar da wannan fasfo. Ita dai kotu, ta yi amfani da sashe na 48 na dokokin zama dan kasa, wadanda suka bayyana cewa duk wani dan Côte d' Ivoire ya yi asarar matsayinsa da zarar ya samu fasfo na wata kasa.

Tidjane Thiam wanda tsohon minista ne, ya bi sahun sauran 'yan adawa kamar tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo, da aka cire sunayensu daga takarar bisa umurnin kotu. Sai dai magoya bayansa sun danganta matakin da manakisar siyasa da nufin kawar da shi daga takara,  duk da cewar jam'iyyar mai mulki ta ce ba ta da hannu a cikin wannan lamarin.