1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceHabasha

Rikicin Habasha na barazanar yaduwa saboda alaka da Sudan?

Ehli David Muntaqa Ahiwa/MAB
October 5, 2026

Sojin Habasha na zargin 'yan gagwarmaya na arewacin kasar da marar alaka da sojojin Sudan, yayin da ake zarginsu da goyon bayan mayakan RSF. Fadace-fadacen da ke faruwa a yankin Kahon Afirka na kara ta'azzara na Habasha.

Rikicin yankin Tigray da ya taba gudana daga 2020 zuwa 2022 ya fara samun hannun cibiyoyin yankin kahon Afirka
Rikicin yankin Tigray da ya taba gudana daga 2020 zuwa 2022 ya fara samun hannun cibiyoyin yankin kahon Afirka Hoto: Yasuyoshi Chiba/AFP/Getty Images

Yayin da sabon fada ke ci gaba a arewacin Habasha, rikicin na kara daukar hankalin kasashen makwabta. Zarge-zargen da Habasha da Sudan da Iritiriya ke yi wa juna na kara fargabar cewa yakin ka iya fadada zuwa wasu sassan Kusurwar Afirka.

Mene ne alakar rikicin Habasha da yakin Sudan, kuma me ya sa kasashen yankin ke zargin juna da hannu a lamarin? Rikicin da ya sake barkewa a arewacin Habasha na kara tayar da hankali, musamman ganin yadda kasashen yankin suka fara zargin juna da hannu a cikin lamarin.

Karin bayani: Rushewar yarjejeniyar zaman lafiya ta Dagula rikicin Habasha

Tun kimanin mako guda, wasu kungiyoyin 'yan tawaye karkashin jagorancin TPLF ta yankin Tigray ke fafatawa da sojojin gwamnatin Habasha. Kungiyoyin na cikin wani kawance na bangarori bakwai masu adawa da gwamnatin Firaminista Abiy Ahmed.

Sai dai sojojin Habasha na zargin Sudan da Iritiriya da Masar da taimaka wa TPLF, zargin da dukkan kasashen uku suka musanta. Sudan ma ta mayar da martani, tana zargin Habasha da taimaka wa mayakan RSF, wadanda ke yaki da sojojin Sudan tun watan Afrilun 2023. 

Kawance mai sarkakiya da ke tsakanin Habasha da Sudan

Firaminista Abiy Ahmed na Habasha da Janar Al-Burhan na Sudan na zargin juna da mara wa tawayen kasashensu bayaHoto: AFP

Masana na ganin wannan musayar zarge-zarge na nuna cewa rikicin Habasha na da alaka da sauran rikice-rikicen da suka dabaibaye Kusurwar Afirka.

Susanne Stollreiter, shugabar ofishin gidauniyar Friedrich Ebert a Habasha, ta ce ko da yake rikicin na cikin gida ne, amma akwai kasashen waje da ke da muradu a cikinsa. Ta yi gargadin cewa idan yakin ya fadada, zai iya jefa yankin baki daya cikin wata babbar tarzoma.

''Akwai bangarori da dama daga ketare da ke da hannu kai tsaye ko a kaikaice, ta hanyar tallafa wa bangarorin da ke rikici ko kuma kare muradunsu a yankin. Wasu daga cikin su na iya cin gajiyar ruruwar rikicin. Saboda haka, lamarin ya wuce rikicin cikin gida kawai. Idan kuma yakin ya kara fadada, akwai yiwuwar ya haddasa babbar tarzoma a yankin, la'akari da dimbin rikice-rikicen da ake fama da su a Kusurwar Afirka.'' in ji Stollreiter.

Karin bayani:Rikici na kara rincabewa a Habasha

Bayan yarjejeniyar zaman lafiya ta Pretoria da ta kawo karshen yakin Tigray a 2022, wasu mayakan Tigray sun tsere zuwa Sudan. Da yakin Sudan ya barke a 2023, wasu daga cikinsu suka kafa rundunar "Army 70", inda suka yi yaki tare da sojojin Sudan na SAF a fafatawarsu da RSF.

A watan Mayu kuma, gwamnatin sojin Sudan ta karbi bakuncin wasu manyan jami'an TPLF da sauran 'yan adawar Habasha a yankin Port Sudan.

A daya bangaren, ana zargin Habasha da kusanci da RSF. A watan Fabrairu, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ana horas da mayakan RSF a wani sansani da ke yankin Benishangul-Gumuz na Habasha. Sai dai kawo yanzu babu wata shaida da ke nuna cewa sojojin Sudan ko RSF sun shiga yakin Habasha kai tsaye.

Rikicin cikin gida na Habasha da ke bazuwa zuwa yanki

Dangantaka ta sake tsami tsakanin Abiy Ahmed na Habasha da Shugaba Isayas Afewerki na IritiriyaHoto: DW

Iritiriya ma na cikin wannan sarkakiyar. A yakin Tigray na 2020 zuwa 2022, ta taimaka wa gwamnatin Abiy Ahmed wajen yakar TPLF. Amma daga baya dangantakar kasashen biyu ta tabarbare.

Karin bayani:Sudan ta zargi Habasha da hannu kan harin da ake kai mata

Wasu masana na ganin Iritiriya na iya marawa abokan adawar Abiy baya saboda fargabar yunkurin Habasha na samun hanyar shiga teku. Sai dai babu kwakkwarar hujjar cewa Iritiriya ta shiga sabon yakin kai tsaye. Ga kuma takaddamar madatsar ruwan GERD, wadda ta dade tana haddasa rashin jituwa tsakanin Habasha da Masar da Sudan kan ruwan Nilu.

A halin yanzu dai, rikicin Habasha bai rikide zuwa yakin kasashen yankin ba. Amma yadda muradun Sudan da Iritiriya da Masar da wasu kasashen Gulf suka cudanya da rikicin, na kara fargabar cewa fadadar yakin ka iya jefa Kusurwar Afirka cikin wata sabuwar tarzoma.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW