Najeriya: Tinubu na kan gaba a jihohi 12
February 27, 2023Talla
Alkaluman sakamakon zaben sun nuna Bola Tinubu na Jam'iyyar APC na kan gaba da kuri'iu miliyan uku da dubu dari bakwai yayin da babban mai kalubalantarsa na Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya ke da kuri'iu miliyan biyu da rabi.
Peter Obi na matsayi na uku da kuri'iu miliyan daya da dubu dari uku. Sai dai kuma Peter Obi na Jam'iyyar Labour ya kada abokin hamaiyarsa na jam'iyya mai mulki a jihar Lagos.
Kawo yanzu dai kimanin kashi biyu cikin kashi uku na jihohin kasar ba a baiyana sakamakon su ba tukunna.
Duk dan takarar da zai zama shugaban kasar sai ya sami mafi rinjayen kuri'iu, ya kuma ya sami kashi daya cikin kashi hudu na akalla jihohi 24.