1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tafiyar "Tinubu Must Go" da "Tinubu Must Stay" na ta da kura

Uwais Abubakar Idris Mouhamadou Awal
October 5, 2026

Kwanaki kalilan bayan bayyanar tafiyar "Dole Tinubu Ya Tafi" da ta samu karbuwa a sassan Najeriya, wata tafiya ta bayyana a matsayin "Tinubu Zama Daram", yayin da ake ci gaba da yakin neman zaben shugaban kasa na 2027.

Shugaba Bola Tinubu na ganin ja da janyewa a yankin neman zaben shugaban kasa
Shugaba Bola Tinubu na ganin ja da janyewa a yankin neman zaben shugaban kasaHoto: Nigerian Presidency/Handout/Anadolu Agency/IMAGO

Yakin neman zaben shugaban kasar Najeriya da za'a yi a badi na daukar sabon salo, inda ‘yan siyasa ke amfani da ayyukan da dan takara ya yi a matsayin abin misali. Wannan ya sanya bullar kungiyoyi biyu na "dole Tinubu ya tafi" da kuma "Tinubu zama Daram". Wannan na sauyi na tasiri a yakin neman zaben shugaban kasa da na dimukuradiyyar kasar.

Najeriya na shirin gudanar da babban zabe na gama gari a farko-farkon 2027, amma hankali yafi karkata a kan zaben shugaban kasar da yafi mamaye fagen siyasar kasar da ma yakin neman zaben da ake yi a yanzu. Farfesa Sadeeq Abba, masanin kimiyar siyasa da ke jami'ar Abuja, ya ce "dole Tinubu ya tafi" da kuma "Tinubu zama Daram" na da ma'ana a guguwar siyasar da ke kadawa a kasar a yanzu a kan batutuwan da ‘yan takara suka aikata.

Karin bayani: Yakin neman zabe ko yaudarar talakan Najeriya?

Hoto: Nasiru Salisu Zango

Tsarin yakin neman zabe na bana ya dogara ne kan batutuwa ko lafuza, sabanin abin da 'yan Najeriya suka saba gani a baya. Tuni, Amnesty International da sauran kungiyoyin kare hakkin jama'a suke nemi gwamnati ta bar 'yan Najeriya su bayyana ra'ayinsu a fagen siyasar kasar don sanin abin da za su zaba.

Dole Tinubu ya tafi da Tinubu zama daram: Me bambanci?

Wannan sauyi ya sanya bullar kungiyoyin siyasa da ke yakin neman zabe a kan dan takrarar shugaban Najeriyar musamman wanda ke karagar mulki, wanda ke son samun zarcewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Bangaren ‘yan adawa ne suka fito da salon "Dole Tinubu Ya Tafi".

Karin bayani: Ko amfani da shugbannin addini zai iya sa Tinubu lashe zabe?

Barrister Abba Hikima, da ya saba fafutuka ne ke jagorantar tafiyar ta siyasa, inda ya ce: "Mun ba 'yan siyasa ba ne ba, amma dole sai ka yi siyasa a Najeriya domin shugabanci musamman ma na siyasa ko kana yi ko ba ka yi ya shiga cikin al'amuranka na yau da kullum. Wannan kasa tamu ta lalace, kowa ya sani, yadda muke rike wuta daga farkon wannan gwamnati zuwa yanzu, su ma abin da za mu yi musu ke nan, ba magana ba ce ta sai wano ko sai wane ba. Mun riga mun zabi Alhaji Atiku Abubakar a yanzu."

Sai dai, kwanakin kalian da wannan tafiya, sai ga shi an yi mata kishiya, inda wata kungiyar ta fito da nata salon na "Tinubu Zama Daram", shin tsoro ne ya sa suka fito da naso salon? Injiya Saidu Ibrahim Uba. jigon a wannan tafiya ya ce: "Mun fahimci abin da gwamnati take yi. Shi ya sa muka fito da tsarin ilimantar da al'umma cewa "Tinubu Zaman Daram", shi ne ya fi alhairi a gare mu."

Me ya sa Amnesty International ta tsoma baki a batun?

Tinubu da Shettima na neman zarcewa a kan kujerar mulkin Najeriya a 2027Hoto: Mubarak Aliyu

Tuni kungiyar kare hakin jama'a ta Amnesty International ta shigo batun don neman a kamanta adalci ga masu yakin neman zabe musamman wadanda ke adawa da gwamnati.

Karin bayani: Za a kaucewa kalaman batacin a zaben Najeriya?

Isa Sanusi, shugaban kungiyar Amensty International a Najeriya ya ce: "Yanzu haka akwai matasa biyar a fursuna. idan aka ci gaba da tauye mutane ana hana su, za mu koma tsarin jam'iyya daya, wanda tsarin mulkin kama karya ne, kuma ba dimukuradiyya ba ne.".

Yakin neman zaben Najeriyar na cike da ban sha'awa inda al'ummar kasar ke kara buda idannu da ya tilasta sauya salon yakin neman zaben tare da bayyana masu inda aka dosa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani
Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW