Kalaman Tinubu kan Gabas ta Tsakiya na shan suka
November 12, 2024Tun daga Lakurawan baya, ya zuwa Boko Haram ta farkon fari, da ma barayin shanu da mutanen da ke cikin tarayyar Najeriya dai, kalma guda da ke bakinsu dai na zaman batu na jihadin gyaran al'umma. Kalmar da ke zaman Larabci, kuma ke kara fitowa fili da dangantakar da ke tsakanin kasashen na Larabawa da kuma sashen arewacin tarayyar Najeriyar.kuma can a birnin Riyad da ke kasar Saudiyya shugaban Najeriyar bai boye tasirin zaman na lafiyar kasashen na Larabawa da batun tsaron da ke Najeriya a halin yanzu .
Kai karshen rikicin Falasdinawa da Yahudawan Isra'ila na bukatar karewa a cikin gaggawa. Kalaman ta shugaba Tinubu dai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriyar ke kallon rawa ta Larabawan a kai tsaye da suna na kungiyar Lakurawa da ke cin karenta har gashinsa can cikin arewacin kasar a halin yanzu. Ustaz Husini Zakariyya dai na zaman daya a cikin jiga jigai na malaman addinan Musuluncin tarayyar Najeriyar.
Zafin kai cikin batun addini, ko kuma kokari na tada hankali, ko bayan kungiyoyi na Musulmi, daga dukka na alamu kasancewar shugaba Tinubun can a birnin na Riyad dai ya burge su kansu malaman addini na Kiristan da ke a Najeriyar.Reverand John Hayab dai na zaman tsohon shugaban kungiyar Kiristocin Najeriyar ta CAN reshen Jihar Kaduna. ''Ko bayan batun tunanin addinin, mafi yawa na makaman da ke a hannu na masu ta'addar Najeriyar dai na fitowa ne daga kasashen arewacin Afirka da ke zaman wani bangaren Gabas ta Tsakiyar.'' To sai dai kuma akwai alamu na neman so irin na zuciya kokarin danganta abin da ke faruwa a Najeriya da rikicin da ke cikin Gabas ta Tsakiya.