1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Cin-hanci

Tinubu ya kafa dambar yaki da cin hanci

July 31, 2023

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada mai bincike na musamman da nufin nazarin badakalar kudi a babban bankin kasar na CBN da kamfanin man fetur NNPC da ragowar cibiyoyi na kudi mallakin gwamnatin kasar.

Shugaba Bola Tinubu na Najeriya na son a ba shi rahoto kan cin hanci a kowane makoHoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Wannan ne karon farko da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna alamun inda bakin gwanatinsa ke shirin karkata ga batun annobar cin hanci da ke zaman ruwan dare a Najeriya. Shugaban ya kaddamar da bincike na musammam na cibiyoyin kudi na gwamnatin kasar da ake yi wa nunin yatsa cikin batun cin hancin. Kama daga babban bankin kasar na CBN ya zuwa kamfanin man kasar na NNPC, Tinubu ya nemi Jim Obazee da ya bankado cuwa-cuwa da halin bera da ake yi a manyan cibiyoyin kudi da ka zama ruhi na tattalin arzikin tarrayar Najeriya.

Matakin nuna rashin sani kan cin hanci

Tsohon shugaban CBN Emefiele na cikin wadanda badakalar cin hanci ta ritsa da suHoto: Sodiq Adelakun/Xinhua News Agency/picture alliance

Tinubu na neman a bankado yawan kudaden haramun da ke hannun jami'ain gwamnati dama 'yan lelen da suka dauki lokaci suna jido suna boyewa, a binciken da ba shi da iyaka, wanda zai rika mika rahotonsa a kowane mako ga shugaban kai tsaye. Duk da cewar an dauki lokaci ana ta korafi da nunin yatsa, amma akwai hasashen yiwuwar kaiwa ga tayar da jami'an tsohuwar gwamnatin APC da ake zargin taka rawa a kokarin wasoso a cibiyoyin kudi.

Kusan Naira Triliyan 37 ne aka fitar a CBN, kuma aka raba su tsakanin jihohi da ita kanta gwamnatin tarraya da sunan bashi. Amma matakin na Tinubu na kara fitowa fili na kokarin raba gari a cikin APC. Kuma sakmakon binciken na Obazee na iya kaiwa ga tada tsohon miki a tsakani na masu tsintsiya. Senata Umar Tsauri na  jam'iyyar PDP ta adawa ya ce ana bukata na bude binciken kafin iya kaiwa ga hukuncin da ke  iya tasiri  bisa harkoki na cibiyoyi na kudi.

Najeriya na asara sakamakon cin hanci

Tsohon shugaban CBN Emefiele na cikin wadanda badakalar cin hanci ta ritsa da suHoto: Sodiq Adelakun/Xinhua News Agency/picture alliance

An dai dade ana ruwa kasa na shanyewa a cikin yakin hancin da ya kalli ta'azzarar wasoso da  dukiyar al'umma, maimakon sauya tunani na yan kasar bisa cin hancin.  Auwal Musa Rafsanjani da ke zaman shugaban kungiyar Transparency in Nigeria mai yaki da cin hancin ya ce  ita kanta sabuwar gwamnatin kasar na neman ta fake da sabon yakin da nufin kau da hankali cikin kasar maimakon aiken sako bisa turbar tarrayar Najeriyar nan gaba.

Tsakanin dalar Amurka miliyan dubu 15 zuwa 18 ne wani rahoto na cibiyar Yiaga ta farar hula ya ce kasar na asara a shekara da sunan kudaden haramun da ake sacewa daga tarrayar Najeriyar zuwa waje.  A wani abin da ke kara fitowa fili ma dai, kasar na asarar da ta haura dalar Amurka miliyan dubu 582 daga cin hanci a cikin shekaru na 'yancin kasar.