1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tinubu ya ce ADC ba ta tsorata shi

April 17, 2026

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce bai tsorata ba da taron hadaka na jam'iyyun siyasa na ADC.

 Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed TinubuHoto: Nigerian Presidency/Anadolu/picture alliance

Ya zuwa yanzun dai jam'iyyar ADC ta adawana shirin rikidewa ya zuwa dashi mai rai guda tara, bayan tsallake siradin rikicin cikin gida da ma adawar INEC ko bayan kokarin hana damar yin taron kasa a farkon mako a Abuja. To sai dai kuma daga dukka na alamu tana da babban shinge kan hanyar kai wa zuwa ga burin karbe mulkin APC ta masu tsintsiya.

Magoya bayan ADC Hoto: Uwaisu Abubakar Idris/DW

Shingen kuma da ke zaman babban dodon kuma shi kansashugaban kasar da 'yan ADC ke son kora. A karon farko na martaninsa ga taron dai shugaba Bola Tinubu ya ce kunnen jaki ba ya shirin ba kura tsoro, don ta gane ba kashi ba ne duk tsoka ce. Wannan dama ce daya tilo a rayuwa ta rushe talauci da jahiLci, da tabbatar da yanci ko bayan kai wa ya zuwa dorewar demokaradiyya.

To sai dai kuma a yayin da shugaban ke buga kirji daga dukka na alamu su ma masu adawar na dada damara a cikin yakin da ke kama da kokarin ko mutuwa ko yin rai. ADC dai na zaman mattatara ta daukaicn adawa ta kasar bayan kanshin mutuwar da daukacin jam'iyyun na adawa suka kalla.

Hoto: Uwaisu Abubakar Idris/DW

Kokari na aiken tsoro, ko kuma gwadakwanjina siyasa, sannu a hankali dai tarayyar Najeriyar ta dau hanyar sake maimaita shekara ta 2014. 'Yan kwanaki da kila wattanin da ke tafe dai na shirin yanke hukuncin ko kada mage zai yanka ta a gwagwarmaya ta neman mulkin tarayyar Najeriyar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani