1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinubu ya rantsar da sabuwar babbar mai shari'a ta kasa

August 23, 2024

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da sabuwar babbar alkali ta kasar mai Shari’a Kudirat Kekere Ekun.

Nigeria Bola Ahmed Tinubu
Hoto: Nigerian Presidency/Anadolu/picture alliance

Mai shari‘a-Kekere Okun dai na  zaman babbar alkalin kasar ta 23,  kuma mace ta biyu da zata jagoranci sashen shari'ar tarraiyar Najeriya da ke bukatar gyara.

Kama daga hukunce hukuncen  da ke karo bisa junansu ya zuwa zargin hanci da kila  sabuwar al‘adar dan mowa da na bora dai, sashen shari'ar tarayyar Najeriyar dai na zaman na kan gaba cikin batun rudanin da ya mamaye daukin kasar.

Wata kiddidigar hukumar kuddidiga ta kasar dai ta ce kowane mutum guda cikin biyar da ya kama hanya zuwa gidan alkalan to ya hadu da matambaya cikin sunan goro. A wani abun da ke tada hankali har cikin gidan alkalan. Barrister Yakubu Mai kyau dai na zaman shugaba na kungiyar lauyoyin tarayyar Najeriyar.

"Kowa ya damu kan tunanin sashen shari'a a matsayin na kan gaba bisa batun  cin hanci. Abun da muke fadi a kungiyar mu ta lauyoyi  shi ne, mu ce duk wani mai zargin cewa wani na karbar hanci, to bai isa ba kawai ya kare shi cikin zargi,  ya kamata yi tamaza ya tabbatar da wannan zargi. Ya samo shaidu da ke tabbatar da wannan zargi, mu kuma mun shirya domin daukar matakin da ya dace. Amma yin zargin ya fi cin hancin ma muni. Mu bama goyon bayan hanci, kuma mun shirya domin yakin hanci a cikin sashen shari'a."

Ko ma ya zuwa ina lauyoyin ke shirin su kai a cikin babban yakin akalla shugabannin sashen shari'ar guda biyu kafin Ariola da ya kare wa'adinsa jiya sun bar aiki a cikin yanayin rudanin hancin.

Cin hancin a cikin gidan shari'ar  tarayyar Najeriyar, a tunanin Barrister Saidu Mohammed Tudun wada da ke zaman shugaban kungiyar lauyoyi na musulmi a kasar, ya kai inna lillahi a halin yanzu.

"Cin hanci da rashawa a matakin shari'a ya kai intaha, ya wuce duk tunanin da muke da shi. Domin za ka ga jaridu da masu bibiyar yadda ake tafi da harkar shari'a da'awarsu ita ce cin hanci yayi katutu a harkar shari'a. Duk in da ka kai tunani, wannan al'amari da muke ciki ya wuce duk in da aka dauke shi sai dai muce inna lillahi wa Inna Ilaihi Raji'un."

Babban aikin da ke gaban sabuwa ta shugabar dai na zaman kallo na abokan takun da ke a bangare na siyasa, tare da ce musu nakin dake iya tasiri ga kokarin tafiyarwar sashen. Aikin kuma da a cewar mai shari'a kekere Okun ke zaman alhaki na babba da yaro cikin kasar.

"Koma menene kasawar da muke gani cikin shari‘ar yau dai, to ita ma shari‘ar wani bangare ne na daukacin al'umma. In muna son mu ga sauyi, to dole ne sauyin ya fara daga kowannemu. Da kuma tunaninmu game da sashen shari'a. Ya kamata mu yi imani kann tsarin. Zamu mai da hankali wajen zabar alkalai, na san yana jawo damuwa mai yawa, haka kuma  zamu kalli tsari na hukuncin alkalai, dama lauyoyi. In Allah yaso ya zuwa karshen wa‘adi na zamu samu sashen shari‘ar da kowa zai alfahari kansa."

Wani kokarin gyaran dai ya kalli shugaban kasar rattaba hannu bisa wata sabuwar dokar da ta ninka yawan albashin alkalan sau gida Uku. Tsarin kuma da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu yace zai ´dada ingantawa da nufin kyautata tsarin mai tasiri.

"Ina son in baku tabbaci cewar, gwamnati na zata ci gaba da baku dukkanin taimako da kuke da bukata domin kyautata jin dadin alkalai da kuma damarsu ta aiki. Zamu kuma cigaba d asauakak tsarin shari'a da kuma karfafa bin dokoki a kasa. Wannan ne yasa na yi gaggawar rattaba hannu kan wata dokar da majalisar tarraya ta gabatar mun. Wadda ta amince da karin kaso 300 bisa albashin alkalai na kasar."

Tinubun dai na zaman mutum na farko da ya tabbatar da cikar kwari a kotun koli ta kasar tare da nada karin alkalai 11 cikin babbar kotun da nufin rage cunkoso da kila saukaka aikin alkalan.