1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinubu ya samu sahalewar gwamnonin APC a zaben 2027

May 23, 2025

Matakin jami'iyyar APC da gwamnoninta na tsayar da Bola Tinubu takara a zaben 2027 na shan martani daga 'yan Najeriya ciki har da na jihohin Katsina da Zamfara , wadanda ke neman a maida hankali kan abin da ke damunsu.

Bola Ahmed Tinubu ya zama zabin gwamnonin APC a zaben 2027
Bola Ahmed Tinubu ya zama zabin gwamnonin APC a zaben 2027Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya da gwamnoninta da 'yan majalisarta a matakin jihohi da na tarayya da sanatoci suka ce sun amince da takarar Shugaba Tinubu a 2027 ne saboda yadda yake tafiyar da kasar kan tsari tare da samar da mafita ga al'ummar kasar. Masana harkokin siyasa na cewa 'yan Najeriya ne ke da wuka da nama wajen zaben shugaban da suke so a shekarar 2027, Kuma suna da ikon yanke hukunci da suka ga dama kamar yadda dimukuradiyya ta tanada.

Karin bayani:  Sauya sheka: Farin jinin APC ko neman biyan bukata?

Malam Sabo Musa Hassan, mataimaki na musamman ga gwamnan jihar katsina kan wayar da kan al'umma ya ce gwamnonin na APC sun yi hangen nesa wajen daukar wannan mataki na amincewa da takarar Tinubu a 2027. Sai dai sauran al'ummar kasar na ci-gaba da tofa albarkacin bakinsu, inda galibinsu ke naman jiga-jigan APC su magance matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya maimakon kula da takara tun kafin a kada kugen siyasa.

Karin bayani:  Ina makomar jam'iyya mai mulki a Najeriya?

Takarar Tinubu na samun goyon bayan 'yan NollywoodHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Masana harkokin siyasa na Najeriya irin su Dr Kabir Umar Musa Yandaki na cewar matakin gwamnonin APC na tsaida Tinubu takara bai zo da mamaki ba, ganin cewar a tarihin kasar babu shugaban da ya taba samar wa gwamnonin lalitar kasar kamar Tinubu. Sai dai ya ce wannan mataki nakasu ne ga dimukuradiyya. Amma a nasa bangaren Sabo Musa, ya musanta alakanta lalacewar tsaro da tattalin arziki ga gwamnatin Tinubu.