1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tinubu ya soke tuhumar cin amanar kasa ga yaran da aka kama

November 4, 2024

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta soke dukkan tuhume-tuhumen da take yi wa kananan yaran nan da ta tsare sakamakon zarginsu da daga tutar kasar Rasha a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

Ministan yada labaran kasar Mohammed Idris shi ne ya sanar da hakan a madadin shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu. Tun da fari dai an tsare yaran sakamakon zarginsu da cin amanar kasa sakamakon daga tutur kasar Rasha wanda laifi ne babba a Najeriyar.

Karin bayani: NAPTIP da Kebbi sun ceto yaran da aka sace 

Mutane 76 ne rundunar 'yan sandan Najeriyar ta gurfanar da su gaban kotu cikinsu har da yara kanana akalla 30, wanda gurfanar da su a gaban kotu a babban birnin kasar Abuja ya haifar da kiraye-kiraye da kuma sukar manufofin gwamnatin  shugaba Tinubu a ciki da wajen kasar kan keta hakkin 'dan adam da kuma azabtar da yaran da aka yi da yunwa da kuma ukuba a inda ake tsare da su.