1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinubu ya yi afuwa ga manyan mutane 175

October 10, 2025

A wani abun da ke iya kai wa ga kace nace a Najeriya, yan kasar da dama na martani kan afuwa da shugaban kasar ya yi wa wasu jiga jigan mutane 175 da ke tsare a gidajen yarin kasar.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Presidencia Villa Abuja

Afuwar da ke zaman irin ta mafi girma a lokaci guda a tarayyar Najeriyar ta kunshi abokai na siyasa da manyan ma‘aikatan gwamnati da 'yan fafutuka.

Kama daga fafutukar neman 'yanci ya zuwa cin hanci da kila halin bera, ko bayan dillancin kwaya, laifuka daban daban mutanen 175 suka tafka da hukunci daban daban cikin tarihi na shekaru kusan 100

Afuwar dai ta shafi mutane daban daban da suka hada da Herbert Macauley daya daga cikin jagororin neman yancin tarayyar Najeriyar a farkon fari ya zuwa wasu 'yan kabilar Ogoni da suka tada kayar baya sakamakon gurbata muhalli.

Duk da cewar dai wasu a cikin masu moriya bisa shirin na gwamnatin sun jima da rasuwa, ana kallon afuwar wasu da suke a raye na iya yin tasiri a fagen siyasar Najeriyar a nan gaba.

Hon Faruk Lawal tsohon dan majalisar wakilai ta kasar kuma daya daga cikin mutanen 175 da suka amfana da afuwar da wasu ke yi wa kallon kokarin sulhunta tsakani da nufin kaiwa ga babban burin siyasa.

Kokarin siyasa komai runtsi, ko kuma neman hidima ta kasa, duk da cewar har yanzu gwamnatin ba ta fitar da daukacin sunayen mutanen 175 da aka yi wa afuwar ba, tuni masu adawar kasar suke fadin da sauran sake

Ko ma menene babban burin yafiyar, akwai tsoron tana iya ta'azzara aiyyukan masu laifi a cikin kasar da ke fafutukar neman mafitar rigingimu iri iri.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani
Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW