1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tinubu zai kulla alaka da Faransa bayan yankar kaunar AES

November 28, 2024

Shugaba Bola Tinubu na Najeriya na wata ziyarar aiki a Faransa, a daidai lokacin da Paris ke kokarin fadada dangantakarta da kasashe rainon Ingila bayan tsamin dangankata da kasashen da ta yi wa mulkin mallaka.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a yayin bude taron yaukaka dangantakar kasuwanci tsakanin China da Afirka (FOCAC) a birnin Beijing na kasar Sin
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a yayin bude taron yaukaka dangantakar kasuwanci tsakanin China da Afirka (FOCAC) a birnin Beijing na kasar Sin Hoto: Greg Baker/AP Photo/picture alliance

Ziyarar ta shugaban Najeriyar na da burin yaukaka diflomasiyyar Faransa da Afirka, wacce a baya bayan nan ke fuskantar yankar kauna daga kasashen da ta yi wa mulkin mallaka irin su Mali da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso, wadanda suka kulla kawance a karkashin kungiyar AES.

Karin bayani: Nijar: Takaddama kan amfani da kudin CFA

Ana sa ran shugabannin kasashen biyu wato Bola Tinubu da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron za su rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama tare kuma da bude taron hamshakan 'yan kasuwar kasashen biyu.

Karin bayani: Kungiyar AES ta soke kudin Roaming na kiran waya 

Faransa dai na bukatar fadada alakarta da Afirka ta fannin kasuwanci duk da kyautata alakarsu da kasashen China da Indiya da kuma Turkiyya.