1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tir da niyar Shekau na sayar da 'yan mata

May 6, 2014

Kungiyar kare hakkin bani adama ta yi kakkausar suka dangane ga barazanar da shugaban Boko haram ya yi na sayar da 'yan matan da aka sace a jihar Borno.

Hoto: Reuters

Hukumar Kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da barazanar da Kungiyar da aka fi sani da Boko Haram ta yi, na sayar da 'yan mata 'yan makaranta da ta sace a garin Chibok na jihar Bornon Najeriya. A lokacin da ya ke bayani a birnin Geneva kakakin shugabar hukumar Rupert Colville, ya ce sun damu matika da furucin da shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya yi ta faifain bidiyo inda ya ce za su yi wa 'yan matan auren dole ko kuma ya sayar da su a matsayin bayi.

Mista Colville ya nunar da cewa matakin da Kungiyar da ke gaggwaryamya da makamai a Tarayyar Najeriya ke niyan dauka ya saba wa dokokin kasa da kasa. saboda haka ne ya bukaci 'yan Boko haram da su saki 'yan matan ba tare da bata lokaci ba, tare da mikasu ga iyayensu.

A Ranar 14 ga watan jiya na Afrilu ne tsagerun na Boko Haram masu kaifin kishin Islama suka sace 'Yan mata 233 daga makarantar garin Chibok na Jihar Borno. Wannan garkuwar ta janyo fusata a ciki da wajen kasar ta Najeriya, inda mutane ke ciki gaba da nuna damuwa kan halin da 'yan mata ke ciki.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Pinado Abdu-Waba