1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Habasha: Tiruneh ya zama sabon mataimakin Firaiminista

February 8, 2024

Majalisar dokokin Habasha ta amince da nadin Temesgen Tiruneh, a matsayin mataimakin firaiminista, a wani garambawul da Abiy Ahmed ya gudanar don karfafa shugabanci a kasar da ke yankin kahon Afrika.

Firaiministan Habasha, Abiy Ahmed
Firaiministan Habasha, Abiy Ahmed Hoto: Fana Broadcasting Corporate S.C.

 Firaiminista Abiy Ahmed, ya kuma amince da nadin  tsohon jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya, Taye Atske Selassie, a matsayin sabon ministan harkokin wajen kasar, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X wanda aka fi sani da twitter.

Abiy, ya bayyana garambawul din a matsayin wani tubalin karfafa shugabancin kasar da ke fama da matsalolin da suka hadar da  dambarwar siyasar yankin da batun karancin abinci da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Nade-naden na zuwa ne a daidai gabar da al'amura suka ki ci suka ki cinyewa a yankin na kahon Afrika da Somaliland ta balle daga Somaliya domin karbe iko da tekun yankin, wanda hakan ke ci gaba da tunzura mahukuntan Mogadishu na kasar Somaliya.