Madugun adawa ya shiga tsaka mai wuya
March 11, 2020'Yan majalisa ne suka shiga shirin cirewa madugun adawa Agbeyome Kodjo na jam'iyyar adawa ta MPDD rigar kariya, bayan da suka zarge shi da laifuka na son tayar da zaune tsaye da yada labaran karya. An dai aika masa da sammaci a wannan Laraba, inda aka nemi ya gurfana gaban wani kwamitin da aka samar kan binciken wadannan zarge-zargen.
Madugun adawan ya sheda ma manema labarai yadda jami'an tsaro suka zagaye gidansa da ke Lome babban birnin kasar. Gnassingbe, mai shekaru 53 da haihuwa ya lashe zaben a wa'adin mulki a karo na hudu. Tun a shekarar 2005 ya dare mulki bayan mutuwar mahaifinsa da ya mulki kasar a tsawon shekaru talatin da takwas.
Dan majalisan da ya fafata da shugaba Faure Gnassingbe a zaben shugabancin kasar, ya kalubalanci sakamaakon zaben da ya ce an tafka magudi cikinsa. Ana bukatar amincewar 'yan majalisan baki daya kafin a sami damar cire masa rigar kariyar.