1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Togo: 'Yan adawa sun kira bore kan dage zabe

April 4, 2024

Jam'iyyun adawa da kungiyoyin fararen hular Togo sun kira zanga-zangar kwanaki uku domin nuna rashin amincewa da matakin dage zaben 'yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi.

Togo Protest gegen die Regierung
Hoto: picture alliance/dpa/AA/A. Logo

Yayin da kasar Togo ta fada cikin turka-turkar siyasa bayan amincewa da sobon kundin tsarin mulki, 'yan adawa da kungiyoyin fararen hula sun kira zanga-zangar kwanaki uku, domin kalubalantar matakin dage zabukan kasar.

Wannan kira na zuwa ne kwana guda bayan sanar da dage zabukan da aka shirya gudarnawa a ranar 20 ga watan Afrilu, wanda gwamnatin kasar ta ce ta yi da nufin bai wa majalisar dokoki damar sake karatun sabon kudin tsarin mulki da aka yi wa gyaran fuska. 

Karin bayani:  Togo: Shugaba Gnassingbe zai ci gaba da mulki

Abin da ya fusata 'yan adawa da kungiyoyin fararen hulan na Togo shine rashin sake tsayar da wata rana domin gudanar da zabukan, sannan kuma suna zargin gwamnatin Faure Gnassingbe Eyadema da yunkurin samar da sabuwar doka wace za ta bai wa 'yan majalisar dokoki damar nada shugaban kasa. 

Karin bayani: An kafa dokar ta baci a Togo

To sai dai tun a shekarar 2022 an haramta yin zanga-zanga a Togo da ke yankin yammacin Afirka, bayan wani hari da aka kai wa babbar kasuwa ta birnin Lome, lamarin da ya yi ajalin jami'in dan sanda guda.