1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Togo: 'Yan adawa za su koma zanga-zanga

Mouhamadou Awal Balarabe GAT
April 18, 2018

'Yan adawar kasar Togo sun kira magoya bayansu zuwa zanga-zangar nuna kyamar gwamnatin Faure Gnassingbe dabra da taron neman sasantawa a karkashin jagorancin Shugaba Nana Akufu Ado na Ghana.

Togo Protest
Hoto: DW

'Yan adawar Togo sun sake tada kayar baya dangane da yunkurin tazarce na shugaba Faure Gnassingbe duk da haramta zanga-zangar da yarjejeniyar da suka cimma da gwamnati ta yi. Jami'an tsaro na ci gaba da amfani da karfi don tarwatsa su a daidai lokacin da kokarin shiga tsakani na shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ke tafiyar hawainiya. 

Tun watan Agustan shekarar 2017 ne jam'iyyun adawa suka fara gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin Faure Gnassingbe na Togo, saboda shi da danginsu sun shafe shekaru 50 suna dafe da madafun ikon kasar. Hasali ma Gnassingbé Eyadema wanda ya dare kan madafun ikon a 1967 ya kayyade wa'adi biyu na shugabanci a cikin kundin tsarin mulki a 1992. Sai dai bayan shekaru goma na mulki, ya sake yi wa wannan doka kwaskwarima inda ya yi tazarce. Sannan bayan da ya mutu a shekara ta 2005, sojoji sun taimaka wa dansa Faure Gnassingbe darewa kan kujerar mulki, kafin daga bisani a yi zabe domin tabbatar da shi a mulki.

Sai dai 'yan adawar na Togo na bukatar komawa kan tsohon kundin tsarin mulki na 1992, wanda ya ke kayyade wa'adin shugabanci biyu na shekaru biyar-biyar. Sannan ba sa so Faure Gnassingbe ya sake tsayawa takara. Saboda haka ne dubban 'yan adawa da shugabannin kungiyoyin farar hula ke fantsama a kan titunan biranen Togo da ke yammacin Afirka. So da yawa ana fuskantar rikici tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro, lamarin da ya sa aka kashe akalla mutane 11. Sai dai zanga-zangar ta fara lafawa daga tsakiyar watan Fabrairu bayan da Nana Akufo-Addo, shugaban kasar Ghana ya shiga tsakani don warware rikicin na siyasa. Wannan tattaunawar ta sa an saki wasu fursunoni siyasa..

Hoto: DW/A. Kriesch


Amma kuma a makon da ya wuce, 'yan adawa sun sake kira da a gudanar da wata sabuwar zanga-zangar bisa zargin gwamnatin Togo da rashin niyar yin gyare-gyare. Sai dai hukumomi sun haramta ta saboda ba a kamalla zaman sulhu da ake yi bisa jagorancin shugaban kasar Ghana ba, a cewar ministan sadarwa na Togo Guy Lorenzo. 

"Duk wanda bai yarda da matakin na gwamnati ba, zai iya kalubalantarsa a kotu. Idan kotu ta ba su dama, to za su iya shirya zanga-zangarsu. Amma 'yan adawar ba su yi haka ba, maimakon haka suka yi burus da haramcin na gwamnati. Wannan ba za mu yarda da hakan ba, saboda kasa ce mai aiki da doka. "

Duk da matakan da jami'an tsaron Togo ke ci gaba da dauka, amma kuma 'yan adawa Togo suka ce babu gudu babu ja da baya a kokarin kawar da Gnassingbe da ya rungumi salon mulkin sai madi ka ture. Alal Hakika ma dai, 'yan sandan kwantar da tarzoma sun bi magoya bayan jam'iyyun adawa har cibiyar jam'iyyar CDPA wajen tarwatsa su, lamarin da Dodji Apevon, Jagora na jam'iyyar (FDR) ya ce bai kamata ba..
 
"A gaskiya idan kuka ga jami'an tsaro dauke da makamai a hedkwatar jam'iyya kun san cewa akwai lauje cikin nadi. Ba zanga-zanga muke gudanarwa ba, amma sojoji sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye, dole ne a iya mamaki abin da ke faruwa". 

Hoto: DW/N. Tadegnon

Shugabannin kasashen hada kai da raya arzikin yammacin Afirka na CEDEAO ko ECOWAS sun bukaci kasar ta Togo da ta hanzarta aiwatar da sauye-sauye da suka dace da mulkin demukaradiyya. A watan ganawar musamman da suka yi sun bukaci shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da takwaransa na Guinea Conakry Alpha Conde da suka ba da shawrawari kan hanyoyin da za a bi wajen warware rikicin siyasar ta Togo.