1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Toni Kroos zai yi bankwana da kwallon duniya

Abdullahi Tanko Bala
May 21, 2024

Dan wasan kwallon kafa na Jamus da Real Madrid midfielder Toni Kroos ya sanar yin bankwana da kwallon duniya a karshen gasar cin kofin zakarun Turai.

Dan wasan kwallon kafa Toni Kroos
Dan wasan kwallon kafa Toni KroosHoto: Pressebildagentur ULMER/picture alliance

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Toni Kroos ya ce zai yi murabus daga wasannin kwararru na duniya bayan wakiltar Jamus a gasar zakarun Turai.

Da yake sanar da haka a shafinsa podcast, dan wasan mai shekaru 34 da haihuwa ya ce ya dade yana tunani mai zufi akan batun kuma ya kammala yanke hukunci a kakar bana zai  yi bankwana da wasannin duniya yana mai cewa wannan hukunci ne mawuyaci.

Toni Kroos wanda ake dauka daya daga cikin kwararrun yan wasa a zamaninsa kuma dan wasan tsakiya mafi shahara ya sami nasarar lashe gasar Bundesliga sau uku da kofin Jamus da kofin zakarun Turai a kungiyar Bayern Munich. Ya kuma sami nasarar daukar kofi har sau hudu a gasar Laliga.