Tony Blair zai gana da shugabannin gabas ta tsakiya
July 24, 2007Talla
A yau ne ake sa ran tsohon firaministan Burtaniya Tony Blair zai gana dabam dabam da shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas da kuma firaministan Israila Ehud Olmert tare kuma da shugaban Israila Shimon Perez.
Blair ya isa yankin ne jiya litinin a ziyarasa ta farko a matsayin jakadan musamman na Amurka da KTT da MDD da Rasha a yankin.
A ranar 27 ga watan yuni aka nada shi wannan matsayi kodayake a wannan ziyara Tony Blair ya zai gana da kungiyar Hamas ba wadda ke rike da zirin gaza.
Kungiyar ta Hamas a nata bangare tace ware ta cikin wannan alamari zai kara rage mutuncin Tony Blair.