1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alakar Faransa da Afirka ta Tsakiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 10, 2023

Cikin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da kuma gidan talabijin din Faransan na TV5 Monde, Shugaba Faustin Archange Touadera na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya ce ba sa adawa da Faransa.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Bangui | Shugaba Faustin Archange Touadera | Faransa
Shugaba Faustin Archange Touadera na Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Barbara Debout/AFP/Getty Images

Tattaunawar da Shugaba Faustin Archange Touadera na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar, na zuwa ne bayan kwashe tsawon shekaru suna takun saka sakamakon alakar da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar ta kulla da babbar abokiyar gabar kasashen Yamma wato Rasha. A cewar Touadera a baya-bayan nan ya karbi sabon jakadan Faransa a kasar, wanda hakan ke nuni da cewa akwai alaka tsakaninsu da kuma yake fatan ta inganta.