Traoré zai ci gaba da mulki a Burkina Faso
October 15, 2022An bayyana Keftin Ibrahim Traoré mai shekaru 34 wanda ya kifar da wata gwamnatin soja a karshen watan jiya a Burkina Faso, a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya.
Traoré ya samu sahalewar wakilan da ke taron kolin kasar da suka fito daga bangarori daban-daban don da nufin sama wa kasar makoma bayan juyin mulki.
Cikin watan Janairun bana ne dai, shi ma Kanal Damiba ya hambarar da gwamnatin Shugaba Roch Marc Christian Kaboré da tsinin bindiga saboda zargin gazawa wajen iya murkushe ta'addanci a kasar.
Kungiyar raya tattalin arzikin yankin yammacin Afirma ECOWAS, na ci gaba da nuna damuwa kan hadarin subucewar dimukuradiyya a Burkina Fason.
Gabanin wannan zabi na sabon shugaba, wasu masu da'awar juyin mulki sun gudanar da zanga-zanga a harabar zauren taron a birnin Ouagadougou, domin nuna goyon bayansu ga Kyaftin Ibrahim Traoré da ya kuduri aniyar mika ragamar mulkin ga wani.