1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Traore zai samar wa Burkina faso tashar makamashin nukiliya

Mouhamadou Awal Balarabe
October 13, 2023

Rasha ta rattaba hannu kan yarjejeniyar gina tashar makamashin nukiliya a Burkina Faso inda kashi daya bisa hudu na al'ummar kasar ba sa samun wutar lantarki. Wannan tasha za ta zama ta biyu a nahiyar Afirka.

Kyaftain Traore ya kulla alaka da kut da kuta da Rasha tun bayan da ya yi juyin mulki
Kyaftain Traore ya kulla alaka da kut da kuta da Rasha tun bayan da ya yi juyin mulkiHoto: Alexey Danichev/AFP

Wannan ci-gaban ya samu ne a daidai lokacin da ake gudanar da taron makon makamashi na kasar Rasha a birnin Moscow, wanda ministan makamashin Burkina Faso Simon-Pierre Boussim ya halarta. Burkina Faso na shigo da kaso mai tsoka na wutar lantarkinta daga makwabtanta Côte d' Ivoire da Ghana.  

Karin bayani:Taron kasashe kan inganta amfani da nukiliya a duniya 

Amma za ta kasance kasa ta biyu ta nahiyar Afirka da za ta mallakin tashar makamashin nukiliya, baya ga wacce Afirka ta Kudu ta malkaka a Koeberg da ke kusa da Cape Town. Dama dai Burkina Faso da ke yankin Sahel da kuma ke karkashin mulkin soja tun shekarar da ta gabata na neman fadada abokan huldarta ciki har da Rasha don samun ci-gaban rayuwa.