1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump: Amirka ta fita yarjejeniyar Paris

Usman Shehu Usman MAB
November 5, 2019

kasar Amirka ta mika takardar janyewa daga yarjejeniyar kare muhalli ta Paris wacce duniya ta cimma. Sai dai kasashe da dama ciki har da Chaina sun nuna takaicinsu a kan wannan mataki na shugaba Donald Trump.

USA Washington Weißes Haus | Donald Trump, Präsident
Hoto: Reuters/T. Brenner

Duk da irin matsin lamba da ya sha daga kawayen Amirka na duniya, amma shugaba Trump ya yi kunnen uwar shegu inda ya fidda Amirka a daya daga cikin manyan yarjeniyoyi na duniya, duk da irin hatsarin da duniya ke fuskanta a yanzu bisa sauyin yananyi. Shugaban na Amirka ya ce Amirka na son tsara yarjejeniyarta ta daban. Ya ce "Za mu fara tattaunawa kan wata sabuwar yarjejeniya da za ta sake shigar da mu a tsarin na Paris, ko kuma wata yarjeneiya ta daban da za ta yi wa Amirka adalci , da 'yan kasuwanta da ma'aikatanta da ma masu biyan harajinta."

A baya dai Amirka ta dage cewa ba za ta shiga yarjejeniyar kare mahalli ba sai manyan kasashe da ke masana'antu irin su China sun shiga. Amma wannan yarjejeniyar ta samu amincewar kasashen China da sauran manyan masu karfin masana'antu na duniya. Don haka ne kasar Chaina ta maida martanin ficewar kasar Amirka.

Chaina ta nuna takaici kan ficewar Amirka daga yarjejeniyar ParisHoto: picture-alliance/MAXPPP/dpa

  Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Chaina GENG SHUANG ya ce: "China na nuna bakin cikin ficewar Amirka daga yarjejeniyar Paris. Mun yi imanin cewa sauyin yanayi matsala ceta bai daya ne da ke tinkarar dukkan bil'Adama. Ya kamata dukkanin  kasashen duniya su hada hannu,ko wace ta yi iyakokarinta don magance matsalar"

Matakin Trump na shan suka a ciki da wajen Amirka

Ita ma Japan wacce ta yi fice wajen kere-kere da masana'antu da ke gurbata mahalli, ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen nuna rashin jin dadinta na ficewar Amirka,Inda aka jiyo babban sakataren majalisar zartaswar kasar Yoshihide Suga, ya na sukar matakin na Amirka.

Ya ce "Sauyin yanayi matsalar duniya ce baki daya, wace al'ummar kasa da kasa ya kamata su magance. Japan ta yi imanin cewa akwai matukar mahimmanci a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar Paris. Bisa wannan bayanan da na yi, mu na nuna bakin cikinmu da cewar Amirka ta sanawar MDD ficewarta daga yarjejeniyar"

Wannan matakin na Donald trump, ko da a cikin kasar ta Amirka ba ko'ina ba ne ya samu karbuwa ba, Inda jihohi da dama suka amince da yarjejeniyar. Kazalika kungiyoyi kare muhalli daga ciki da wajen Amirka sun yi Allah wadai da matakin janyewar kasar da kuma nuna irin hatsarin da ke tattare da hakan ga duniya.

Manyan jami'an Amirka kamar Al Gore na fafutukar kare muhalliHoto: picture-alliance/AP Photo/E. Risberg

 David Waskow, daraktan cibiyar yaki da sauyin yanayi ta kasa da kasa ya ce : "Ina ganin shugaba Trump a zahiri tunaninsa ya  nuna sam bai kusa da sanin abin da ke faruwa a cikin Amirka ba. Sama da kashi uku ciki hudu na Amirkawa na goyon bayan yarjejeniyar Paris. Akwai 'yan kasuwa da birane cikin Amirka wadanda suka ce sun rungumi yarjejeniyar Paris. A yanzu muna da jihohi 25 a Amirka da suka hada kai wajen yaki da muhalli"

Ga kungiyoyin fafutika ficewar Amirka ba karamar illa ba ce domin yanzu lokacin da duniya ke bukatar daukar matakan kare muhalli fiye da ko wane lokaci ne, inda a watan Satumban bana aka yi zafin rana da ba'a taba ganin irinsa ba ko kuma an jima da ganin irinsa a kasashen duniya da yawa.