An gudanar da taron addu'o'i ga Charlie Kirk
September 22, 2025
Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana fitaccen matashin nan mai ra'ayin 'yan mazan jiya da ke rajin tabbatar da dimukuradiyya a Amurka, Chalie Kirk a matsayin wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga 'yancin Amurka. Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wajen taron tunawa da kuma addu'o'i ga matashin. Dubun dubatar mutane ne suka halarci taron addu'o'in sanye da jajjaye da kuma fararen riguna.
Karin bayani: An harbe matashin da ke da ra'ayin mazan jiya a Amurka
Abokan Kirk da masu ra'ayin 'yan mazan sun yaba wa matashin na zama abin koyi a kan riko da addinin Kirista da ya samar da wata kafa da za su ci gaba da raya ta. An bindige matashin mai shekarar 31 yayin da yake tsaka da yin jawabi ga dandazon dalibai a jami'ar jihar Utah a ranar 10 ga watan Satumbar 2025.