Trump da Erdogan sun tattauna kan Libiya
January 16, 2020Talla
A ranar Lahadi mai zuwa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel z ata karbi bakuncin shugabannin kasashen Turkiyya da Rasha da Amirka da Birtaniya da Faransa da kuma Italiya domin lalubo mafita a rikicin kasar Libiya, bayan kin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin da ke yaki da juna a Libiyan suka yi bayan kammala taron sulhu a Rasha a ranar Litinin din data gabata.
Yayin tattaunawar shugabannin kasashen Turkiyar da Amirka sun tabo yanayin da kasar Siriya ke ciki da zanga-zanga a Iran bayan rikitowar jirgin kasar Ukraine.