Trump da EU sun gaza fahimtar juna kan Rasha
May 25, 2017Shugaba Donald Trump na Amirka da manyan jami'ai na Kungiyar Tarayyar Turai sun gagara kallon juna kan batutuwa da suka shafi sauyin yanayi, da harkokin kasuwanci da ma alaka da Rasha kamar yadda shugaban majalisar Donald Tusk ya bayyana a wannan rana ta Alhamis bayan sun gana Trump.
Shi dai Trump ya sosa zuciya ta jami'an na EU bayan da ya nuna goyon bayansa karara ga shirin ficewar Birtaniya daga Kungiyar ta EU, ya dai gana da Tusk da Shugaban hukumar ta Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker a lokacin ziyararsa ta aiki karon farko zuwa birnin na Brussels.
A cewar Tusk sun samu baki yazo guda kan wasu batutuwa wasu kuma sun raba gari:"Mun tattauna kan batutuwa da suka shafi harkokin kasa da kasa da tsaro, mun amince kan batutuwa da dama musamman kan yaki da ta'addanci, bakinmu yazo guda kan Ukraine amma batutuwa da suka zama hanyamu a bude suke har yau su ne sauyin yanayi da kasuwanci da alaka da Rasha, batutuwa ne da ba zan ce komai kai tsaye kansu ba 100 bisa 100 a wannan rana."