1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump da Harris na shirin tafka mahawara kan manufofinsu

September 8, 2024

'Yan takarar shugabancin kasar Amurka Donald Trump da Kamala Harris za su fuskanci juna a ranar Talata mai zuwa domin yin mahawara kan mabambantan manufofinsu a game da makomar Amurkar.

Kombobild | Donald Trump und Kamala Harris
Hoto: Alex Brandon/AP/picture alliance und Mat Otero/AP/dpa/picture alliance

Za a gudanar da mahawarar da ake sa ran za ta kasance mai zafi a birnin Philadelphie da ke jihar Pennsylvania da ake dauka a matsayin jiha mafi mahimmaci a Gabashin Amurka da ka iya canja akalar zaben da za a gudanar a watan Nowamban da ke tafe.

Karin bayani: Kalubalen da ke gaban Harris na yin nasara a zaben Amurka

Tuni ma aka cimma daidaito a tsakanin ofisoshin yakin neman zaben Donald Trump da abokiyar hamayyarsa Kamala Harris a game da sharrudan mahawarar wacce gidan talabijin na ABC zai jagoranta.

Karin bayani: Trump ya yi alkawarin kawo karshen rigingimun kasa da kasa

Sai dai a wannan karo masu jagorantar maharar ne kadai ke da damar yin tambayoyi ga masu zawarcin kujerar fadar mulkin ta White House, sannan kuma ba za a raba jigon batutuwan da mahawarar za ta tabo ga 'yan takarar ba.