1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump zai yi tozali da Machado a fadar White House

Abdoulaye Mamane Amadou
January 9, 2026

A karon farko tun bayan da ta sadaukar masa da kyautar Nobel ta zaman lafiya da aka ba ta, 'yar adawar Venezuela Maria Corina Machado za ta gana da Shugaba Trump a daidai lokacin da kasarta ke cikin rudanin siyasa

Maria Corina Machado da ta lashe kyautar Nobel
Maria Corina Machado da ta lashe kyautar Nobel Hoto: Lise Åserud/NTB Scanpix/dpa/picture alliance

A farkon makon gobe shugaba Donald Trump zai gana da madugar 'yan adawar Venezuela kuma wadda ta lashe lambar yabo ta zaman lafiya Nobel, Maria Corina Machado a birnin Washington inda ya ce yana dokin ganawa da ita.

Trump na dokin yin tozali da Maria Corina Machado

Trump ya sanar da cewar Machado za ta iso Washington nan ba da jimawa ba, kuma yana matukar sa ran ganinta domin in gaishe ta, saboda ya ji cewar tana son haka. A baya Shugaba Trump ya bayyana cewar Machado ta taba kiransa har ma ta sadaukar da lambar yabonta gare shi. "Ya ce Matar da ta samu lambar yabo ta Nobel a wannan karon ta kira ni yau, ta ce min ta karbi lambar yabon ne a madadina, domin a cewarta ni ne na fi cancanta da lambar yabon. Wannan abu ne mai kyau matuka."

Shugaba Trump ya taba nuna rashin jin dadin yadda aka ba Machado lambar yabo ta Nobel

Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: Alex Brandon/AP Photo/dpa/picture alliance

Shugaban Amurka ya taba caccakar matakin kwamitin da ke bayar da lambar yabo t Nobel, kuma hakan ya haifar da rikici na siyasa bayan ya so a bashi lambar yabon bisa abin da ya kira kokarin samar da zaman lafiya da ya a duniya, wanda ya ba shi samun goyoyn bayan wasu shugabannin duniya da ‘yan majalisar Amurka, amma kuma kwamitin bayar da kyautar ya amince da bai wa Machado lambar saboda aikin da ta yi wajen fafutukar tabbatar da hakkin dan'Adam da saukake zaman lafiya a Venezuela. Wasu bayanai  na fadar White House sun soki hukumar Nobel, suna cewa ta fi sanya siyasa a gaban zaman lafiya.

Machado ta sadaukar da lambar yabonta ga Trump

Duk da haka, Machado ta nuna cewa ta karbi lambar ne bisa nuna godiya ga Trump ta kuma sadaukar da ita a ga Shugaba Trump da kuma al'ummar Venezuela saboda goyon bayansu amma ba za a iya sauya ko ba wa wani lambar Nobel da aka riga aka ba wa wani ba bisa ka’ida.

An saki 'yan hamyya da ke tsare a gidajen fursuna

A gefe guda gwamnatin Venezuela ta saki wasu dumbin fursunonin siyasa da ke tsare ciki har da fitaccen dan adawar Maduro kuma tsohon dan takara a zaben shugaban kasar Enrique Marquez. Sai dai shugabar riko ta Venezuelar Delcy Rodriguez ta ce kasar ba za ta kasance karkashin wata kasa ba.