SiyasaJamus
Trump da Xi Jingpin sun cimma matsayar kasuwanci
October 30, 2025
Talla
Trump wanda ya kammala rangadi a kasashen Asiya, ya fara yada zango ne a Koriya ta Kudu a ranar Litinin , inda ya bai wa Koriya ta Kudu izinin kera jirgin yaki na ruwan mai amfani da makamashin Nukiliya, sannan kuma ya cimma matsayar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Shugaban ya bayyana hakan ne bayan ganawa da shugaban Koriya ta Kudu Lee Jae-Myung da wasu shugabannin yankin a ziyarar da ya kai kasar.
Koriya ta Kudu ta ce tana bukatar makamashin Nukiliya don sarrafa jiragen karkashin ruwa da za a yi amfani da su wajen sa ido kan jiragen ruwan Koriya ta Arewa da China.
Karin Bayani: Trump ya rage wa China haraji