1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya zargi FBI da kokarin kala masa sharri

August 10, 2022

Wasu majiyoyi a Amirka na cewa kotu ce ta sahale wa FBI din kutsawa gidan Donald Trump domin binciken ko ya boye wasu takardun sirri na gwamnati.

USA Donald Trump America First Agenda Summit In Washington
Hoto: Drew Angerer/Getty Images

Tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya koka a kan yadda hukumomi suka hana shi sake shiga katafaren gidansa da ke bakin teku a Florida tun bayan samamen da jami'an hukumar binciken manyan laifuka ta FBI suka kai gidan. Tsohon shugaban ya yi zargin hukumomi da yunkurin ajiye wani abu a cikin gidan domin a kala masa sharri. 

A watan Fabrairun da ya gabata rahotanni sun ce an gano akwatuna 15 makare da muhimman takardun gwamnati da Mr. Trump ya wuce da su gidansa maimakon ya bar su a Fadar White House.

Hakan na zuwa ne a yayin da Donald Trump din ya bayyana dazu a ofishin atoni-janar na birnin New York domin ya yi karin bayani a kan wata badakalar kasuwanci da iyalansa ke yi. Sai dai Mr. Trump ya ce haka ya yi ''funfurus'' yaki magana a ofishin domin 'yancin da yake da shi na dan kasa na ya yi magana ko ya yi shiru. Kafin yanzu Trump din ya nemi kotu ta haramta gayyatarsa amma kotun ta ki aminta da hakan.